20 Yuni 2021 - 12:07
WHO Ta Jinjinawa Kasar Guinea Kan Murkushe Ebola

Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta sanar da kawo karshen annobar Ebola a kasar Guinea, ‘yan watanni bayan da cutar ta sake bulla a kasar.

ABNA24 : An bayyana cewa murkushe annobar ta ebola, bai rasa nasaba da kwarewar da kasar ta samu a yaki da annobar a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016.

Da yake sanar da hakan, a wani biki da aka shirya jiya Asabar jami’in hukumar ta WHO, a Guinea Alfred Ki-Zerbo, ya ce yana farin cikin sanar da kawo karshen Ebola a kasar ta Guinea.

Cutar ta Ebola ta dai sake bulla ne a yankin Nzerekoro dake kudu maso gabashin Guinea a karshen watan Janairu.

WHO, ta kuma jinjinawa hukumomin kiwon lafiya na Guinea akan kokarin da sukayi wajen murkushe annobar.

342/